
FIYE DA ƘIMA wato "RUSHING" [HEAVY BLEEDING]
â–“â–“â–“â–“â–“â–“â–“â–“â–“â–“â–“â–“â–“â–“â–“â–“â–“â–“â–“â–“â–“â–“â–“â–“
Kamar yadda in aka dafa dankali yake laushi tuɓus ta yadda ko yatsa kasa ka dirza ɓawonsa zaka ga ya saluɓe nan da nan, ko kuma saboda ma tsabar shan wuta zaka ga ya sassaluɓe ya fashe.....
Toh kwatan-kwacin abinda ke faruwa kenan a cikin mahaifar ƴaƴa Mata wato (uterus) a yayin haila. Haka mayanin bangon mahaifarsu ke ɓamɓarowa tare da saluɓowa ya zubo kamar yadda maciji ke saɓa... wanda hakan ke haifar da fitar wannan jinin wanda ake kira jinin haila bayan salubowarsa.
Sannan hakan zai sa ku fahimci yadda period keda tsananin zafi, zogi da ciwo, domin in dankali yasha wuta ka daukesa a hannu kaima kasan me ka taɓa wajen azabar zafi, Toh amma haka su Mata jikinsu ke karɓar wannan zogin, shiyasa ba banza ba wasu ke murqususu, wadu ma basa iya mikewa sosai sak sui tafiya saboda azaba yadda kowa agidan sai yasan lokacin hailar wance yayi, domin kowa da yanayin irin yadda jikinsa ke isar masa da saƙon zogi ko zafi.
____________________________________________________________________________
Zanyi ƙarin haske ne akan zubar jini sosai fiye da ƙima dakan faru da wasu matan yayin haila.
A ƙa'idance bai kamata ace yayin haila Mace ta fitar da jinin da yafi cikin sirinjin allura me lambar biyar (5ml syringe
UNDER MAINTENANCE