Banbanci Tsakanin Computer Science Da Computer Engineering! Assalamu Alaikum yan'uwana dalibai wannan karen nazo maku da sanin banbanci tsakanin Computer Science Da Computer Engineering. Da farko ma menene ita kanta Computer din..?😀 Wato a tarihin gina Computer (Generation of Computer) ya kasance tun daga generation na farko (1940) lokacin da ake amfani da Vacuum tube, generation na biyu ake amfani da Transistors, na ukku akayi amfani da Integrated Circuit, na hudu wanda muke amfani da Microprocessor, na biyar wanda muke amfani dashi kuma ake amfani dashi har nan gaba shine: Artificial Intelligence. Computer itace na'ura mai kwakwalwa wanda take tace bayanai ta kuma fitar dasu, (Processing data) sannan kuma ta ajiye bayanai (Storing information). Wadda aka kirkire ta domin sauqaqewa mutane aiki da al'amurran yau da kullun.. To idan aka kirata da Computer Engineering fa..? Wato a takaice ma'anar kalmar Enginering shine: Kirkirar abubuwa ta hanyar hikima da basira da kuma wayo, wato wani bangare ne da ake amfani da bincike da ilimi na kimiyya wajen kirkirar duk wasu abubuwa da zasu sauqaqewa dan adam aiki, Engineering hanya ne da ake amfani da ilimin kimiyya da lissafi domin a tabbatar da samar da abinda zai taimaka wajen ingantawa da sauqaqewa al'umma ayyukansu na yau da gobe.. To kunga anan zamu iya cewa ma'anar Computer Engineering shine: Karatu ne na sanin ilimin kimiyyar na'ura mai kwakwalwa tareda yadda ake hada ta da ingantata da sanya mata fasaha kala-kala wanda zai kawo sauqi wajen gudanar da ayyukan mu na yau da gobe, to kaga kenan shi Computer Engineer dole yasan ciki da wajenta zai iya budeta kuma ya maidata sannan ya gyarata, ko ya inganta ta (upgrading) ta hanyar canza mata wasu sassan na jikinta dan sabunta ta tayadda zata zama na zamani, haka zalika kuma ilimin Engineer na computer ya kasu kashi biyu: 1. Akwai Hardware Engineering: wato ilimin sassan Computer na zahiri kamar su: ita kanta Computer din (CPU), Motherboard, Hard disk, Ram, Rom, Monitor, Keyboard, Mouse, da dai sauransu. Sai kuma ilimi na 2. Software Engineering: wannan kuma ilimi ne da ya shafi (software) wato manhaja kamarsu Operating System, Application software, da Utilities. To idan kuma aka kirata da Computer Science fa..?😀 Computer Science a takaice: Ilimi ne na sanin kimiyyar Computer tunda daga asalinta, zuwa me za'a iya yi da ita, kuma tayaya za'a iya sarrafata tareda bata umarnin yin wasu abubuwa da yarenta (Programming languges) domin kirkirar wata manhaja kokuma wani abunda zai sauqaqewa Al'umma aiki na yau da gobe, wanda yawancin aikin Computer Scientist ya ta'allaka ne ga fahimtar Theory nata da practical dinta tareda sani sosai akan Languages nata kamar irinsu: PHP, Python, C-Family, SQL, CSS, Java, da sauransu domin dasu zai bata umarni domin gabatar da wani Aiki (Program) kokuma kirkirar wata fasaha domin tabbatar da cigaban computer da zamani.. Wannan shine takaitaccen banbancin Computer Engineering da kuma Computer Science.. Daga ALPHOLTAWY DIGITAL INFORMATION TECHNOLOGY (ADIT) Ku kasance tare dani naku Ismail Hussaini Adamu (ALPHOLTAWY) Domin neman Karin Bayani Kushiga kai tsaye dan magana da ni ALPHOLTAWY.design.blog Ko Ku kirani Akan Numbata 09047958802