Karatun Kimiyyar Kwamfiyuta (Computer Science) (Hasashen Masana yanuna Cewar ilimin Computer matsakaici zai Zama wajibi ga Dai-Da-ikun mutane domin gudanar da rayuwar su ta yau da kullum...) •✓Abubuwan da Darasin Yaqunsa: 1•Bayanin Bsc. Computer 2•Bayanin Bangarorin Computer(area of Specialized) 3•Tarihin ginuwar ilimin Computer 4•Bayanin Computer Engineering 5•Bayanin Software Engineering... Asha Karatu Lafiya ’Yan Computer! Kimiyyar kwamfuta ita ce nazarin fasahar kwamfuta, duka hardware da software! ilimin na'ura mai kwakwalwa fage ne Mai fadin Gaske Wanda yahada bangarori daban-daban; Ƙwarewar da ake buƙata duka biyun ce Wato Software Da Hardware. ana buƙatar ilimin a kusan kowanne masana'antu a duniyar dogaro da fasaha ta yau! Don haka, fannin ilimin na’ura mai kwakwalwa ya kasu kashi-kashi a cikin guraben Karatu Ko Jami’o'in Mu! wadanda akasarinsu cikakkun fannoni ne na musamman Masu Zaman kansu. Fannin kimiyyar kwamfuta ya mamaye sassa da dama a fadin duniya. Dalibai za su zaɓi ƙwarewa daban-daban dangane da aikace-aikacen da ake so a digiri na kimiyyar kwamfuta, Ko da yake mafi tsananin ƙwarewa da samun horo yana faruwa a matakin digiri, na Farko; sanin ainihin menene ilimin kimiyyar kwamfuta (da kuma inda sha'awar ɗalibi ta faɗo cikin wannan fage mai faɗi) yana da matuƙar mahimmanci ga sanin yadda ake karatun kimiyyar kwamfuta ga Dalibai a Yanzu; B.Sc. Computer Science; An tsara shirin a cikin Kimiyyar Kwamfuta tare da mahimman darussa waɗanda ke ba da fa'ida da zurfi a fagen, tare da ƙaƙƙarfan bincike, a ɓangaren. ya hada da darussa a fannin kimiyya da lissafi; bukatun ilimi na gabaɗaya a cikin ɗan rayuwar adam da kuma jerin zurfafan kwasa-kwasan kwamfuta na musamman. Babu Lokacin Batawa Domin Fadawa Dalibai Bangaren Dazasuyi Aiki idan Sun karanci Bangaren Na Computer Domin kuwa ita "Sha Kundum Ce!" inde Computer kayi Kuma dagaske kayi karatun Kuma ka iya Computer to Aiki Kam saide kabawa Wasu Dan kaima zaka iya Qirqirar Ayyukan Yi. Nan Gaba Kadan Hasashen Masana yanuna Cewar ilimin Computer matsakaici zai Zama wajibi ga Dai-Da-ikun mutane domin gudanar da rayuwar su ta yau da kullum! Ga kadan Daga Cikin Bangarori da Dalibi Ze iya Neman Ƙwarewa a Bangaren Ilimin Kwamfiyuta: (areas of specialization) •Applied Mathematics •Digital Image/ Sound •Artificial Intelligence •Microprogramming •Bioinformatics •Networks And Administration •Computer Architecture Networks •Cryptography •Computer Engineering •Operating Systems •Computer Game Development •Robotics •Computer Graphics •Simulation And Modeling •Computer Programming •Software Development •Software Systems •Data Management •Web Development •Design Database •Parallel Programming •iOS Development •Mobile Development •Memory Systems •Computational Physics •Banbanci Tsakanin Computer Science Da Computer Engineering: Wato a tarihin gina Computer (Generation of Computer) ya kasance tun daga generation na farko (1940) lokacin da ake amfani da Vacuum tube, generation na biyu ake amfani da Transistors, na ukku akayi amfani da Integrated Circuit, na hudu wanda muke amfani da Microprocessor, na biyar wanda muke amfani dashi kuma za’ake amfani dashi har nan gaba shine: Artificial Intelligence! Computer itace na'ura mai kwakwalwa wanda take tace bayanai ta kuma fitar dasu, (Processing data) sannan kuma ta ajiye bayanai (Storing information). Wadda aka kirkire ta domin sauqaqewa mutane aiki da al'amurran yau da kullun. To idan aka kirata da Computer Engineering fa.? Wato a takaice ma’anar kalmar Enginering shine: Kirkirar abubuwa ta hanyar hikima da basira da kuma wayo, wato wani bangare ne da ake amfani da bincike da ilimi na kimiyya wajen kirkirar duk wasu abubuwa da zasu sauqaqewa dan adam aiki, Engineering hanya ne da ake amfani da ilimin kimiyya da lissafi domin a tabbatar da samar da abinda zai taimaka wajen ingantawa da sauqaqewa al'umma ayyukansu na yau da gobe! To kunga anan zamu iya cewa ma'anar Computer Engineering shine: Karatu ne na sanin ilimin kimiyyar na'ura mai kwakwalwa tareda yadda ake hada ta da ingantata da sanya mata fasaha kala-kala wanda zai kawo sauqi wajen gudanar da ayyukan mu na yau da gobe, to kaga kenan shi Computer Engineer dole yasan ciki da wajenta zai iya budeta kuma ya maidata sannan ya gyarata, ko ya inganta ta (upgrading) ta hanyar canza mata wasu sassan jikinta dan sabunta ta tayadda zata zama na zamani, haka zalika kuma ilimin Engineer na computer ya kasu kashi biyu: 1. Akwai Hardware Engineering: wato ilimin sassan Computer na zahiri kamar su: ita kanta Computer din (CPU), Motherboard, Hard disk, Ram, Rom, Monitor, Keyboard, Mouse, da dai sauransu. Sai kuma ilimi na 2 Software Engineering: wannan kuma ilimi ne da ya shafi (software) wato manhaja kamarsu Operating System, Application software, da Utilities. •To idan kuma aka kirata da Computer Science fa..? Computer Science a takaice: Ilimi ne na sanin kimiyyar Computer tun daga asalinta, zuwa me za'a iya yi da ita, kuma tayaya za'a iya sarrafata tareda bata umarnin yin wasu abubuwa da yarenta (Programming languges) domin kirkirar wata manhaja kokuma wani abunda zai sauqaqewa Al'umma aiki na yau da gobe, wanda yawancin aikin Computer Scientist ya ta'allaka ne ga fahimtar Theory nata da practical dinta tareda sani sosai akan Languages nata kamar irinsu: PHP, Python, C-Family, SQL, CSS, Java, da sauransu domin dasu za'a bata umarni domin gabatar da wani Aiki (Program) kokuma kirkirar wata fasaha domin tabbatar da cigaban computer da zamani. Daga ALPHOLTAWY DIGITAL INFORMATION TECHNOLOGY (ADIT) Ismail Hussaini Adamu (ALPHOLTAWY) Domin neman Karin Bayani alpholtawy.design.blog 09047958802 Alpholtawy@gmail.com